Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta Nijeriya ta kama wasu muggan makamai da ake zargin ana shirin shigo da su daga Jamhuriyar Nijar zuwa hannun ’yan bindigar da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
A cewar rahoton Zagazola makaman da ya wallafa a shafinsa na X, jami’an DSS sun kama makaman ne a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, a Dawakawa da ke ƙaramar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.
Rahoton ya bayyana cewa, an ƙwato bindigogin AK-47 guda 21 tare da manyan bindigogin PKT guda huɗu da kuma magazin guda 825.
Rahotanni sun ce waɗanda ake zargin sun yi amfani da raƙuma ne wajen safarar makaman domin kauce wa jami’an tsaro a kan iyakar Najeriya da Nijar, sai dai cikin ikon Allah, ba su samu damar tsallakewa da kayan ba.