Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na jam’iyyar APC, ya sanar da wasu sauye-sauye da suka shafi tsarin sadarwa da yaɗa labaransa, inda ya bayyana cewa, daga yanzu mutuane uku ne kaɗai za su riƙa yi. magana a madadinsa.
A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa waɗanda aka amince su riƙa magana da yawunsa su ne Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen, wato, Sanata Abdulaziz Yari da Ministan Ma’adanai, Dele Alake, da kuma Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris.
Haka kuma, sanarwar ta ƙara da cewa sauran mutanen da aka naɗa a baya a matsayin masu magana da yawun kwamitin za su koma ƙarƙashin ƙaramin kwamitin yaɗa labarai a matsayin mambobi.
Kwamitin ya kuma ce zai riƙa zaɓar waɗanda suka dace domin su yi magana da yawunsa a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.