Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da ƙara wa'adin neman tallafin karatu na "Katsina State Merit-Based Scholarship Scheme" zuwa ranar Juma'a, 13 ga watan Nuwamba, 2026, domin bai wa Ɗaliban da suka cancanta ƙarin damar neman wannan tallafi.
Shirin, wanda aka ƙaddamar ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, zai samar da tallafi ga Ɗalibai 1,700, inda kowace daga cikin Ƙananan Hukumomi 34 za ta samu kaso na Ɗalibai 50.
Tallafin zai ƙunshi kuɗin makaranta, rajista, sauran kuɗaɗen karatu da aka amince da su, da alawus na shekara-shekara a makarantun da aka ware. Haka kuma, ya haɗa da shirye-shiryen HND a fannonin Injiniya.
Yayin cika wannan tallafi, ba a buƙatar JAMB ga masu neman gurbin kwalejojin ilimi guda biyu da shirin ya tanada, amma dole ne su cika sauran sharuɗɗan shiga makaranta.
Waɗanda ba su da takardar shaidar zama ɗan asalin Ƙaramar Hukuma (Indigen) za su iya amfani da takardar gabatarwa daga Shugaban Ƙaramar Hukuma ko wakilinsa da aka amince da shi, bisa tantancewa.
Zaɓen waɗanda za su amfana zai kasance bisa cancanta da adalci.
Masu sha'awar wannan dama za su iya shiga shafin yanar gizon nan da ke ƙasa domin cike takardun neman tallafin
🌐 https://katsina34meritscholarship.com
Domin ƙarin bayani ko taimako, ana iya tuntuɓar Dr. Aminu Salisu Tsauri: 08037446501 ko kuma Hon. Isah Miqdad AD Saude: 07064607578
Gwamnatin jihar na kira ga iyaye da shugabannin al'umma da jami'an Ƙananan Hukumomi da su wayar da kan Ɗaliban da suka cancanta, musamman waɗanda ke yankunan karkara, domin cin gajiyar wannan dama.