Kasar Najeriya ce a Kan Gaba Wajen Gurfanar da Wadanda Ake Zargi da Ayyukan Ta'addanci

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da ke kan gaba a duniya wajen gurfanar da waɗanda ake zargi da ta'addanci da kuma yanke musu hukunci, lamarin da ya ce yana nuna ƙudurin gwamnatinsa na yaƙi da ta'addanci ta hanyar ayyukan soji da kuma tsarin shari'a.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja, yayin buɗe taron shekara-shekara na 2026 na Hukumar Leƙen Asiri ta Tsaro (CDI), inda Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya wakilce shi. Ya ce haɗa matsin lambar soji da gurfanar da masu aikata laifuka a kotu na da matuƙar muhimmanci wajen wargaza ƙungiyoyin ta'addanci da hana su sake farfaɗowa.

Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa a ƙarƙashin gwamnatinsa, an kashe tare da kama manyan jagororin ƙungiyoyin ta'addanci huɗu daga cikin takwas da aka gano. Ya lissafa matakan da aka ɗauka kan shirin faɗaɗa ayyukan ISWAP a kudancin ƙasar ƙarƙashin Ahmed Ohida, kashe babban jagoran IS, Abu Bilal Mainuki, a watan Mayun 2026, da kuma kama Abu Barra na ƙungiyar Ansaru da Mamuda na Mahmudawa a shekarar 2025.

Ya yaba wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro bisa sadaukarwar da suke yi, tare da jaddada buƙatar ƙara haɗin gwiwa wajen tattara bayanan sirri da amfani da fasahohin zamani domin magance matsalolin tsaro. Tinubu ya kuma buƙaci mahalarta taron da su samar da dabarun da za su ƙara inganta ayyukan leƙen asiri da tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro a Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post