Tsohon Gwamnan Legas Babatunde Fashola ya Bayyana Dalilin da ya sa Aka Cire Tallafin Man Fetur, Tare da Yin Gargadi ga Batun Dawo da Tallafin

Bankin Duniya ne ya sharɗanta cire tallafin man fetur kafin ba Najeriya bashi

Tsohon gwamnan Legas, Babatunde Fashola, ya ce Bankin Duniya ya shaida wa gwamnatin Najeriya cewa ba za ta sake samun tallafin kuɗi daga bankin ba matuƙar ba ta cire tallafin man fetur ba.

Fashola, wanda ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV ranar Talata, ya ce cire tallafin ya zama wajibi sakamakon matsin tattalin arziƙi da kuma tanaje-tanajen dokokin harkokin man fetur.

Ya ƙara da cewa, Najeriya na kashe kusan kashi 90 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta wajen biyan basussuka a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari, lamarin da ya sa ci gaba da biyan tallafin man fetur ya zama babban nauyi ga ƙasar 

A cewarsa, bai kamata gwamnati ta dawo da tallafin ba saboda matsin lambar jama'a, yana mai ƙalubalantar masu son dawo da shi da su bayyana inda za a samo kuɗin gudanar da shirin.

Tsohon ministan ya amince cewa cire tallafin ya ƙara tsadar rayuwa tare da jefa iyalai cikin matsin tattalin arziƙi, amma ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ɗaukar matakai domin rage wa jama'a raɗaɗin hakan.

Ya lissafa sauye-sauyen haraji da shirin lamunin karatu na NELFUND da ƙarin albashi da aka yi wa ma'aikata da kuma amfani da iskar gas wajen zirga-zirga a matsayin wasu daga cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka don sauƙaƙa wahalhalun da ake ciki.

Fashola ya kuma bayyana cewa hauhawar farashi ya ragu daga sama da kashi 30 zuwa kusan kashi 14 cikin 100, yana mai gargaɗin cewa dawo da tallafin na iya kawo cikas ga ci gaban da aka samu.

Post a Comment

Previous Post Next Post