Barawon da ya Saci Wayoyin Miliyoyin Naira a Farm Centre, Barci ya Sace shi a Wurin, ya Gurfana a Gaban Kuliya

Wani matashin mai suna Abba Abubakar ya gurfana a gaban kotun Shari'ar Musulunci da ke post office ƙarƙashin jagorancin alƙali Abdullahi Yusuf ɗauke da takardar tuhume-tuhumen shiga waje bada izini ba tare da ɓalle shago da kuma Sata.

Lauyar gwamnati mai gabatar da ƙara barista Ummi Habib Almajir ita ce ta gabatar da shi kuma an karanta masa ƙunshin tuhume-tuhumen, amma ya musanta.

Alƙali ya waiwayi mai gabatar da ƙara, wadda ta nemi da a ɗaga shari'ar zuwa wani lokaci domin ta samu damar gabatar da shaidunsu a gaban kotun.

Kotun ta amince, kuma kotun ta bayar da damar a yi belinsa, sai dai har zuwa lokacin tashi daga kotun babu wanda ya zo domin yin belinsa.

Shi dai Abba, ana zarginsa da zuwa kasuwar waya ta Farm Centre inda ya ɓalle wani shago ya ɗebi wayoyi na sama da naira miliyan biyu, an bayyana shagon a matsayin mallakar Alhaji Gazzali.

Bayan satar wayoyin, sai bacci ya ɗaukeshi har gari yawaye aka zo aka same shi da kayan da ya sata a tare dashi, wanda daga nan ne 'yansanda suka yi gaba da shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post