Kwamitin Majalisar Wakilai ta Najeriya mai kula da albarkatun ma'adinai ta bai wa babban kwamandan hukumar tsaron fararen hula (NSCDC), Farfesa Ahmed Abubakar Audi wa'adin sa'o'i 24 ya bayyana a gabanta.
Kwamitin ya bayyana cewa, ana son ganin kwamandan bisa zarge-zargen almundahanar kuɗi da kama mutane ba bisa ƙa'ida ba da kuma karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba, waɗanda ake zargin jami'an rundunar Mining Marshals da aikatawa.
Kwamitin ya kuma buƙaci ƙarin bayani kan kisan wani jami'in NSCDC mai muƙamin mataimakin Sufeto, Agada Levi Agada, wanda ake zargin wasu jami'an hukumar sun kashe a wani wurin haƙar ma'adinai.