Ministan Kudi ya Bayyana Damuwarsa Kan Yadda Ake Yada Bayanan Boge, Wadanda Suke Korar Masu Zuba Hannun Jari a Kasar

Labarai marasa daɗi da ake yaɗawa game da Najeriya na korar masu zuba jari da ƙwararru - Oyedele

Ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arziƙin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya ce yaɗa munanan labarai da bayanan ƙarya kan Najeriya na hana masu zuba jari shigowa ƙasar, tare da tilasta wa ƙwararrun ’yan Najeriya neman ayyukan yi a ƙasashen waje.

Oyedele ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron 2026 World Public Relations Forum da aka gudanar a Abuja.

Ya ce irin waɗannan labarai na rage amincewar masu zuba jari da tattalin arziƙin ƙasar, ƙara kuɗin jari da kuma kawo cikas ga ci gaban kasuwanci.

Ministan ya ce amincewa da gwamnati da cibiyoyinta na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziƙi.

Ya ce, “Amincewa ita ce ginshiƙin dukkan sauran kuɗaɗe. Idan aka samu amincewa, jama’a za su ba da haɗin kai, masu jari za su zuba kuɗaɗensu, sannan kasuwanci zai bunƙasa.”

Oyedele ya bayyana cewa kalaman da ake yaɗawa kamar “Najeriya ta lalace” da “Najeriya damfara ce” na iya shafar yadda masu zuba jari ke kallon damar kasuwanci a ƙasar.

Sai dai ya jaddada cewa hakan ba yana nufin gwamnati na hana jama’a sukar shugabanni ko fallasa gazawarsu ba, yana mai cewa yakamata a riƙa yaɗa bayanai cikin gaskiya da riƙon amana.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda kafafen sada zumunta ke taimakawa wajen yaɗa bayanan ƙarya, musamman sakamakon amfani da fasahar basirar wucin gadi wajen ƙirƙirar hotuna, muryoyi da takardu na bogi.

Ministan ya buƙaci kafafen yaɗa labarai, masu tasiri a kafafen sada zumunta da ƙwararrun hulɗa da jama’a su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su.

Ya ce, “Ku tabbatar da gaskiyar bayani kafin yaɗa shi, kuma idan kun yi kuskure, ku gyara shi da ƙarfin da kuka yaɗa labarin tun da farko.”

Ya ƙara da cewa ingancin labarin da ake yaɗawa game da Najeriya ya kamata ya dogara da ainihin abin da jama’a ke fuskanta, ba yawan tallan da gwamnati ko kamfanoni ke yi ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post