Wani ƙwararren masanin binciken likitanci ya bayyana cewa akwai alamun da ke nuna cewa Jeffrey Epstein, attajirin Amurka da aka samu da laifin cin zarafin yara mata ta hanyar lalata, mai yiwuwa an kashe shi ne a gidan yari a shekarar 2019, maimakon ya kashe kansa kamar yadda rahoton hukuma ya bayyana.
Masanin, mai suna Dr. Michael Freeman, wanda shi ne babban editan mujallar Journal of Forensic and Legal Medicine, ya bayyana hakan ne bayan shafe lokaci yana nazarin bayanan binciken gawar Epstein da kuma hotunan da aka samar masa. Ya gabatar da sakamakon bincikensa a birnin London ranar Litinin.
Freeman ya shaida wa gidan talabijin na CBS News cewa raunin da aka samu a jikin Epstein bai yi daidai da wanda ake samu idan mutum ya rataye kansa da niyyar kashe kansa ba. A cewarsa, idan aka haɗa dukkan alamomin da aka gano, sun fi nuna yiwuwar an shake Epstein ne daga bayansa ta amfani da wani ɗan siririn kyalle da aka ɗaure ƙulli.
Epstein ya mutu ne a ranar 10 ga watan Agustan 2019, bayan an same shi a rataye a cikin ɗakinsa na gidan yarin Metropolitan Correctional Center da ke birnin New York, yayin da yake tsare yana jiran shari'a kan zargin safarar mutane domin lalata da su. A lokacin, yana fuskantar tuhume-tuhume masu tsanani da suka shafi cin zarafin yara mata da safarar mutane domin lalata.
Sai dai binciken gawar da aka gudanar a lokacin ya tabbatar da cewa Epstein ya kashe kansa ne ta hanyar ratayewa. Ofishin Babban Likitan Binciken Gawarwaki na Birnin New York (New York City Office of Chief Medical Examiner) ya kuma sake jaddada cewa yana nan daram a kan wannan matsaya duk da sabon ikirarin da Freeman ya yi.
Mutuwar Epstein ta daɗe tana jawo ce-ce-ku-ce a duniya, musamman saboda alaƙar da yake da ita da manyan attajirai, 'yan siyasa da wasu fitattun mutane. Wasu na zargin cewa an kashe shi ne domin hana shi tona asirin mutanen da ake zargi da hannu a ayyukan lalata da cin zarafin yara mata. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da waɗannan zarge-zargen ba.
Wani abin da ya ƙara tayar da tambayoyi game da mutuwarsa shi ne rashin aikin kyamarorin tsaro da ke wajen ɗakinsa a ranar da ya mutu. Wani rahoton Ma'aikatar Shari'a ta Amurka na shekarar 2023 ya tabbatar da cewa gidan yarin yana da matsaloli da suka daɗe suna damun tsarin kyamarorinsa.
Ɗan'uwan Epstein, Mark Epstein, ya sake yin kira da a buɗe sabon bincike kan mutuwar ɗan'uwansa bayan sabon bayanin da Freeman ya gabatar. Ya nuna rashin gamsuwarsa da hukuncin da aka yanke tun farko kan musabbabin mutuwar.
Sai dai duk da sabon binciken da Freeman ya gabatar, har yanzu babu wata sabuwar matsaya ta hukuma da ta sauya hukuncin cewa Epstein ya mutu ne ta hanyar kashe kansa. Saboda haka, batun ko an kashe shi ko kuwa ya kashe kansa yana ci gaba da kasancewa abin muhawara.
