Mutane da yawa musamman waɗanda suke da wata 'yar dama a hannunsu sai da yawa suna neman hanyar da za su rena ka ne, musamman idan suka gan ka da shigar al'ada, tun ba ta Bahaushe ba.
Wannan wani labari ne, na wani bawan Allah da wani abu ya faru da shi A Airport na Nairo da ke ƙasar Kenya, mutumin ya ce, na je wani wurin da ake canjin kuɗi domin yin canji in samu na kashewa har ma da na yin tsaraba haɗi da guzuri, sai na samu wata mata wadda take bayar da canji. Bayan da ta karɓi fasfo nawa sai ta kalli cikin idanuna, sai ta fara zuba kamar kanari cikin harshen Ingilishi ta fara da cewa, in cire takunkumin fuska (facemask) duk da na san ba jami'ar tsari ba ce, haka na bi umarnin ta na cire, don dai a zauna ƙalau.
Ya ƙara da cewa, ko da ganin ta samu kaina, sai kawai ta ci gaba da cewa, "Na ga ka yi kama da 'yan Taliban". Buɗar bakina sai na ce da ita su waye 'yan Taliban? Sai ya dawo min da tambayar ba ka san 'yan Taliban ba? Sai na amsa mata da cewa, ke kin san su ne? Ko ke mamba ce?
Nan take ta hau ɓari, tare da waiwayawa sashen da CCTV kamata take, ta sa hannu tana rufe baki da hanci, ko da na lura da cewa, za a iya jiyo tattaunawar tamu ta CCTV sai na kwance bakin zare, na sake cewa, Ko ke budurwar wani ɗan Taliban ce.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta sauya fuska tare da faɗin, "Don me za ka ce haka? Me ya haɗa ni da su?" Cikin dariya na ce: "To idan ba ki da alaƙa da su, a ina kika san su har kike kwantanta ni da su?" Sai ta ka da baki ta ce: "Ah, ai labarinsu yana nan a kan intanet. Ba ka duba intanet ne?" Ni kuwa na ce: "Idan ina duba intanet me haɗina da mutanen da ba ni da alaƙa da su?" Daga ƙarshe dai ta ba Ni canjina. Bayan ta ba ni canjin kuɗin tare da fasfo nawa, sai na ce mata: "Na gode budurwar ɗan Taliban."
Tags
Labarai