Gwamnatin ƙasar China ta bayyana jin daɗi da godiya ga hukumomin Najeriya bisa yadda suka nuna kulawa da kuma saurin ɗaukar mataki wajen ceto ‘yan kasarta da wasu ‘yan Najeriya bayan an yi garkuwa da su a wani yankin ƙasar.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta China ta fitar, ta ce tana yaba wa ƙoƙarin hukumomin tsaro na Najeriya musamman Ofishin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da kuma Gwamnan Jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, bisa yadda suka jagoranci aikin ceto mutanen cikin lumana.
A cewar sanarwar: “China na godiya ga gwamnatin Najeriya bisa jajircewa da saurin amsawa wajen kare rayukan ‘yan kasarta. Wannan abu ne da ya ƙara ƙarfafa dangantakar abota tsakanin ƙasashen biyu.”
Gwamnatin China ta ce tana sa ran ci gaba da haɗin gwiwa da Najeriya wajen tabbatar da tsaro da kare lafiyar ‘yan ƙasashen biyu, musamman ma a fannin zuba jari da kasuwanci da ke ƙara bunƙasa a yankin kudu maso yammacin Najeriya.