Sauro Ya Bayyana A Ƙasar Iceland a Karon Farko

Sauro Ya Bayyana A Ƙasar Iceland a Karon Farko a Tarihi

Cibiyar Tarihin Halittu ta Iceland ta karɓi samfurin sauron da aka samu a ƙasar Iceland karo na farko a tarihi domin ci gaba da bincike. Matthias Alfredson fitaccen  masanin halittun nan shi ne ya tabbatar da cewa lallai wannan sauro ne.

An ambata cewa sauron yana jure yanayin sanyin da ake samu a Arewacin Turai, ana kiran irin wannan sauro da suna Culiseta annulata.

Post a Comment

Previous Post Next Post