Fasinjoji a Filin Jirgin Saman Muhammadu Buhari na Ƙasa da Ƙasa da ke Maiduguri, Jihar Borno, sun makale na sa’o’i a ranar Litinin bayan wani matuƙin jirgin Max Air ya ƙi tashi saboda bashin kuɗaɗen haƙƙoƙinsa da kamfanin bai biya ba.
Shaidu sun ce fasinjoji fiye da 100 sun riga sun hau jirgin kuma sun shirya tafiya lokacin da matukin ya ƙi yin aiki, yana zargin yana bin kuɗi da saura haƙƙoƙi.
“Mun riga mun zauna a kujerunmu, sai aka ce mu sauka daga jirgin,” in ji wani fasinja. “Daga baya muka ji cewa matuƙin ya ƙi tashi saboda bashin albashi.”
Fasinjojin da suka cika da haushi sun jira na dogon lokaci a zauren tashar jirgin kafin a sasanta lamarin. Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya tashi da misalin ƙarfe 2:00 na rana.
Daraktan Harkokin Jama’a da Kare Masu Amfani da Sabis na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (NCAA), Mista Michael Achimugu, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hukumar ba ta tsoma baki ba domin an warware matsalar a cikin gida.