Dalilan Da Ke Sa Har Yanzu Boko Haram Ke Ci Gaba Da Kai Hare-Hare

Masana kan harkokin tsaro a Najeriya sun yi ƙarin bayani kan dalilan da suka sa har yanzu ƙungiyar Boko haram ke ci gaba da kai hare hare kan jam'ain tsaron ƙasar.

Boko Haram

Duk da iƙirarinda gwamnatoci da hukumomin tsaro a Najeriya ke fitar wa masu nuna yadda aka karya ƙarfin ƙungiyar, an ga yadda daga lokaci zuwa lokaci Boko Haram ke iya kai hari kan jami'n tsaron Najeriya.

Masanan sun ce mayƙan boko Haram na kai hare haren ne saboda yadda suke amfani da sabbin dabaru da na fasaha da suke samu daga ƙungiyoyin da suke ƙwance da su da ke irin ayyukansu a afrika da ma sauran ƙasashen duniya.

Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya) ya yi wa BBC ƙarin bayani kan yadda yake kallon sake dawowar hara haren na Boko Haram.

Ya ce dama yaƙi irin wanda Najeriya ke yi da Boko Haram abu ne mai wahalar shawo kai idan aka yi la'akari da cewa abu ne na aƙida.

Post a Comment

Previous Post Next Post