Filasdinawan Gaza Sun Koka Kan Rashin Sauyi Duk Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

 Isra’ila Ta Ci Gaba Da Hana Shigar Da Agaji a Yankin.

Duk da sanarwar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da Hamas, jama’ar yankin Gaza sun ce ba su ga wani sauyi a rayuwarsu ba, yayin da Isra’ila ta ci gaba da hana shigar da kayan agaji da abinci cikin yankin.

Wasu mazauna Gaza sun shaida wa kafafen watsa labarai cewa matsin tattalin arziki da karancin abinci, magani, da man fetur sun ci gaba da ta’azzara, lamarin da ya sa rayuwa ke kara wahala. “Sun ce an ce zaman lafiya ya dawo, amma mun ci gaba da jin yunwa da tsoron sabuwar harba makami,” in ji wani mazaunin Khan Younis.

Hukumar agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) ta bayyana cewa tana da damuwa matuƙa da yadda Isra’ila ke ci gaba da toshe hanyoyin shiga Gaza, tana mai cewa hakan yana hana kai tallafi ga dubban mutane da ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, rikicin siyasa da rashin amincewa tsakanin ɓangarorin biyu na cigaba da kawo cikas ga komawar zaman lafiya ta gaskiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post