Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rashin abinci mai gina jiki ba matsalar lafiya kawai ba ce, har ila yau barazana ce ga tattalin arziki da ci gaban ɗan adam.
Gwamna Lawal ya faɗi haka ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da Shirin Zamfara State Nutrition 774 Initiative, inda ya ce kafa Majalisar Jiha kan Abinci Mai Gina Jiki wata muhimmiyar dama ce da za ta kawo sauyi wajen gina al’umma mai ƙarfi ta hanyar mayar da hankali kan lafiya da jin daɗin yaran Zamfara.“Ba za mu iya gina Jihar Zamfara mai tsaro, ɗorewa da cigaba a kan tushe na rashin abinci mai gina jiki ba,” in ji Gwamna Lawal. “Zuba jari a cikin kwanaki dubu na farko na rayuwar yaro shi ne babban jarin da za mu iya yi domin makomar jiharmu.”
Ya bayyana cewa Shirin Nutrition 774 (N774) yana amfani da tsarin da ke haɗa fannoni da dama kamar lafiya, noma, ilimi, walwalar jama’a da tsaftar muhalli (WASH), don tabbatar da ciyar da al’umma gaba.
Lawal ya ce shirin ya yi daidai da “Rescue Agenda” na gwamnatinsa, wanda ke mai da hankali wajen ƙarfafa mata da bunƙasa shirye-shiryen gina ƙauyuka.
Ya kuma sanar da kafa Majalisar Jiha kan Abinci Mai Gina Jiki, wacce ta ƙunshi manyan kwamishinoni da shugabanni, masu ikon tsara manufofi, daidaita ayyuka da kuma sa ido kan dukkan shirye-shiryen abinci mai gina jiki a fadin jihar.