Sojojin Najeriya Sun Harbe Dan Bindiga Abu AK Bayan Sun Kamashi

 An Kashe Shi Lokacin Da Ya Yi Yunkurin Guduwa.

Rahotanni daga yankin Arewacin Najeriya sun tabbatar da cewa sojojin ƙasar sun kama wani sanannen ɗan bindiga mai suna Abu AK, kafin daga bisani su harbe shi yayin da yake ƙoƙarin tserewa daga hannunsu.

Wani majiyin tsaro ya bayyana cewa rundunar ta kai samame kan mafakar ‘yan ta’adda inda aka yi artabu mai zafi, wanda ya kai ga kama Abu AK da wasu abokan aikinsa. Bayan ɗan lokaci, ɗan bindigar ya yi ƙoƙarin guduwa daga hannun jami’an tsaro, abin da ya sa aka buɗe masa wuta, kuma ya mutu nan take.

Hukumar tsaro ta ce wannan nasara ta nuna cewa sojoji na ci gaba da samun galaba kan ‘yan ta’adda, tare da tabbatar da tsaro a yankunan da rikice-rikice suka daɗe suna addabar su.

Post a Comment

Previous Post Next Post