Majalisar Wakilai A Nijeriya Za Ta Tabbatar Da Daurin Rai da Rai Ga Masu Aikata Lalata Da Kananun Yara

 Majalisar Dattawa ta gabatar da wani muhimmin ƙudurin doka da zai bayar da damar yanke hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata ƙananan yara ba tare da yiwuwar biyan tara ba.

Majalisar Wakilai

Wannan mataki na daga cikin sauye-sauyen da aka yi wa Dokar Laifuka ta shekarar 2025.

Shugaban Majalisar, Opeyemi Bamidele, wanda ya jagoranci muhawarar kan kudurin, ya ce sauye-sauyen na da nufin karfafa dokokin kare yara da kuma kawar da nuna bambanci a kan jinsi wajen gurfanar da masu laifukan lalata.

A halin yanzu, hukuncin shekaru biyar a gidan yari ake yanke wa wanda aka kama da laifin lalata yara, amma a ƙarkashin wannan kuduri idan aka amince da shi, hukuncin rai da rai zai fuskanta.

Bugu da ƙari, Majalisar ta kuma gabatar da hukuncin shekaru 10 a gidan yari ga masu aikata fyaɗe.

Post a Comment

Previous Post Next Post