Shafin yanar gizon ya jaddada rawar da Pi zai taka a biyan kuɗaɗe tsakanin ƙasashe, da kuma dacewarsa da ƙa’idar zamani ta ISO 20022. Miliyoyin “Pioneers” a duniya sun nuna ƙwarin guiwa da wannan labari.
Pi Core Team ta tsara tafiyarta zuwa matakai guda uku:
Mataki na farko: kafin Nuwamba 2025
Mataki na biyu: ran 22 Nuwamba 2025, lokacin aikace-aikacen ISO 20022
Mataki na uku: bayan ƙaddamarwa, wato lokacin faɗaɗa amfani da shi zuwa ƙasashe da ƙungiyoyi daban-daban
Ranar 22ga Nuwamba 2025 ta zama muhimmi domin ita ce ranar ƙarshe da aka sanya ga duk bankuna da cibiyoyin harkokin kuɗi su sauya zuwa tsarin ISO 20022. Bayan wannan nasara, Pi na shirin ƙaddamar da kayan aikin biyan kuɗaɗe tsakanin ƙasashe da za su yi tasiri ga hukumomin gwamnati.
Sai dai, har yanzu akwai buƙatar a Sai dai, har yanzu akwai buƙatar a duba takamaiman hujjoji masu zaman kansu daga bankuna ko gwamnati da ke nuna cewa Pi za ya riga ya fara aiki a matsayin kuɗin dijital na hukuma. Ƙarfafa wannan ra’ayi zai dogara ne kan haɗin guiwa daga manyan cibiyoyin kuɗi da tsarin da za a bi don tabbatar da amfani da shi.