“Ban Ma Tunanin Abinda Ya Faɗa Ba, Kuma Ban Damu Ba” - De La Fuente.
Kocin ƙungiyar ƙasar Sifaniya, Luis de la Fuente, ya yi martani mai zafi kan zargin da kocin Jamus, Hansi Flick, ya yi masa cewa bai tafiyar da matashin ɗan wasa Lamine Yamal yadda ya kamata ba.
De La Fuente ya ce:“Hansi Flick ya ce ban kula da Lamine yadda ya dace ba? Ban ma tuna abin da ya faɗa ba, kuma gaskiya ban damu da shi ba.”
Maganganun kocin Sifaniya sun zo ne jim kaɗan bayan da aka yi ƙorafe-ƙorafe kan yadda ake sarrafa ƙarfin matashin ɗan wasan Barcelona, wanda ke taka rawa mai mahimmanci a ƙungiyar ƙasa duk da ƙarancin shekarunsa.
Wannan martanin ya haifar da cece-kuce a tsakanin magoya baya, inda wasu ke ganin De La Fuente ya yi watsi da sukar da aka yi masa, yayin da wasu kuma ke goyon bayansa cewa ya fi kowa sanin yadda zai tafiyar da ‘yan wasansa.