Kamar yadda rohoton jaridar Daily Nigerian ya ruwaito, Atiku Abubakar ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya yi alƙawarin janye wa “matashin ɗan takara” a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar da sanarwa a ranar Talata yana cewa an yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuskuren fassara.
“Ya zama wajibi a fayyace wasu kuskuren fahimta da suka taso daga rahoton hirar da Mai girma, Atiku Abubakar, ya yi da BBC Hausa, kamar yadda wasu sassan kafafen yaɗa labarai suka bayar,” in ji shi.
“Bayan dubawa sosai kan bidiyo da kuma rubutaccen kwafin hirar – duka a harshen Hausa na asali da kuma fassarar Ingilishi – an tabbatar da cewa a ko’ina cikin hirar, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa bai faɗi hakan ba ko nunawa ko ma alamar cewa yana da niyyar janye wa wani.
“Abin da Atiku Abubakar ya faɗa a bayyane kuma ba tare da wata ruɗani ba shi ne cewa matasa da sauran masu sha’awar neman takarar shugaban ƙasa suna da ’yanci su shiga gasar.
“Ya ƙara jaddada cewa idan wani matashi ya yi nasara ta hanyar zaɓen fidda gwani na gaskiya, zai ba shi goyon baya ba tare da wani jinkiri ba."
