Ministan tsaron Isra’ila ya gargadi kimanin mutane rabin miliyan da ke cikin birnin Gaza cewa idan ba su bar wurin ba, za a dauke su a matsayin “’yan ta’adda” ko “magoya bayan ’yan ta’adda.”
Wannan barazana ta tayar da hankula a cikin al’umma, yayin da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam suka bayyana ta a matsayin hukunci na haɗin guiwa wanda ya haramta wa fararen hula haƙƙinsu saboda kawai suna zaune a gidajensu.
Wasu iyalai sun yi yunƙurin yin tafiyar haɗari zuwa kudancin Zirin Gaza, amma da dama ba su iya ba. Tsofaffi, marasa lafiya da kuma iyalan da ke da ƙananan yara sun ce barazanar bama-bamai ya yi yawa don su iya barin wurin. Ko da waɗanda suka isa kudanci, sukan fuskanci cunkoso da rashin wurin zama.
Ga iyalai da dama, rayuwa a Gaza City ta zama gwagwarmayar tsira. Amma da Isra’ila ke ƙara zurfafa hare-haren kasa da kuma lalata muhimman ababen more rayuwar jama’a, damar tsira na ƙara raguwa a kullum.