Tauraruwar Ƙwallon Ƙafa Ta Halarci Ibada Bayan Komawarta Ƙungiyar Al Hilal.
Ƴar wasan ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Asisat Oshoala, ta wallafa hotunanta a shafukan sada zumunta a cikin ɗakin Ka’aba yayin da take gudanar da ibadar Umara a ƙasar Saudiyya.
Oshoala, wacce ta shahara a duniya saboda bajintarta a fagen ƙwallon ƙafa mata, ta koma sabon ƙungiyar Al Hilal da ke Saudiyya a bana, inda ta rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu.
Tauraruwar dai ta bayyana farin cikinta da samun damar gudanar da ibadar Umara tare da nuna godiya ga Allah bisa sabuwar dama da ta samu a ƙasar Saudiyya.
Hotunan da ta raba sun ja hankalin masoya da magoya bayanta, inda da dama suka yi mata fatan alheri a sabon tafarkin rayuwarta na addini da kuma ƙwallon ƙafa.