Matatar mai ta Ɗangote ta yi tayin biyan albashin ma’aikatan da ta kora na tsawon shekaru biyar ba tare da aikin komai ba, domin kaucewa yiwuwar ɓarna daga hannunsu, amma ƙungiyar ma’aikata ta PENGASSAN ta ƙi amincewa da hakan. Majiyoyi sun shaida wa Premium Times cewa duk da damuwar gwamnati kan nauyin kuɗin, Ɗangote ya dage cewa hakan ya fi sauƙi a gare shi fiye da barin ma’aikatan da bai amince da su ba a cikin masana’antar tasa.
Sai dai PENGASSAN ta zaɓi a mayar da ma’aikatan wasu sassan kamfanonin na Ɗangote tare da ba su cikakken albashi, abin da aka amince da shi bayan sulhu da gwamnatin tarayya ta shiga tsakani. Matatar Ɗangoten ta kori ma’aikatan ne bisa zargin aikata ɓarna da kawo barazana ga tsaro ga aikin masana’antar.
Wannan mataki ne da ya tayar da rigima, inda PENGASSAN ta umarci mambobinta su janye ayyuka, kafin daga baya a cimma matsaya ta sulhu. Shugaban na PENGASSAN, Festus Osifo, ya yi gargaɗi cewa za a koma yajin aiki idan Ɗangote ya karya yarjejeniyar.
Tags
Tattalin Arziki
