Mai daraja gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya ƙaddamar da motocin safa-safa na Zamfara State Mass Transit. An laƙaba wa motocin tambarin jihar Zamfara da kuma na sunan Bazamfara.
Gwamnan ya ƙaddamar da su ne ranar 2ga Oktoba, 2025. Yayin ƙaddamar da motocin ya ce sun yi la'akari da irin buƙatocin al'umma na sufuri kamar ƴankasuwa masu neman lafiya, ƴanmakaranta da sauran al'umma.
Waɗannan motoci suna ɗauke da haɗin intanet da ake kira Wifi da fasinjoji kan iya amfani da shi har zuwa wuraren da za a isa. Gwamnan ya ce motocin za su riƙa zuwa jihohi kamar Sokoto, Kaduna, Kano, da Gombe da sauransu.
Gwamnan ya yi kira ga jama'a da su kula da waɗannan motoci domin kuɗinsu na jiha aka yi amfani da su wajen sayensu. Kuma ya ce sun wayar da kan direbobi da su kasance masu kyakkyawar mu'amula da fasinjoji yayin da suke gudanar da aikin.