Sanata Friday Benson Konbowei, wanda ke wakiltar Bayelsa Central a majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasikar sauya shekar Sanata Konbowei kafin ƙarewar zaman majalisar a ranar Alhamis.