Gudunmowar Musulmin Farko A Harkar Lafiya

Mutane da dama sukan ɗauka cewa, aikin likitanci na zamani daga Turawan Yamma ne, don haka ba shi da wata alaƙa da addini saboda ba su riƙi addini sosai ba. Haka kuma tun a zamanin kunne ya girmi kaka, wato wajen shekaru kusan dubu goma da suka wuce, an san harkar magani a duniya, a ƙasashe irinsu Misra da Farisa da Sin da kuma Indiya. Amma magunguna ne na saiwoyi da ganyayyaki da ’yan dabaru a wancan lokacin. Daga bisani ne ilmin zamani ya ɓullo daga ƙasashen yamma.

Musulmin Farko Da Ya Fara Bada Gudunmowa A Harkar Lafiya

Likitancin wannan zamani ya samo asali ne daga kasar Girka tun a shekarun 2000, kafin zuwan Annabi Isa AS (2000 BC), ta hannun wani mai suna Hippocrates, wanda bai da wani addini. Ya zauna a kan karan kansa, ya karanci ɗan Adam ciki da bai, da ’yan magungunan da kowane sashen jiki ya fi buƙata, ya riƙa rubutawa yana kuma koyar da tunanin nasa, ɗaliban nasa ma suna ƙara tasu fahimtar. A haka ilmin sanin dan Adam ya bunkasa har ta zo sai da aka kafa jami’a babba a wannan ƙasa, ta koyar da aikin likita, wadda ta zamo cibiyar biɗar ilmi daga ko’ina a Nahiyar Turai.

Yayin da Musulunci ya shiga ƙasashen yamma ta ƙasar Andalusiya (Spain) a shekarun 650 bayan zuwan Annabi Isa, ya tarar da irin wannan ilmi na likitanci amma bai rushe shi ba. Wasu daga cikin Musulmin wannan zamani sai suka dukufa suka shiga makarantun koyar da aikin likitanci suka koya, suka kuma kara nasu sanin da fahimta a kan wadancan na Turawan. Kuma har yau wasu daga cikin nasu karin na nan a cikin manhajar ilmin, ba a rushe su ba. Wani abin haushi da Turawan yamma na yanzu suke yi shi ne, na boye sunayen Musuluncin wadancan mutane, suna sa musu nasu na Turanci, wai don a ce su ma nasu ne.

Ga kaɗan daga cikin irin waɗannan mashahuran Musulmin da suka fara ƙirƙiro abubuwan da har yanzu ake amfani da su: An ba da duka sunayensu na ainihi da na Turancin da kuma zamanin da suka zo:

Muhammad bin Zakariyya Al-Rhazi: Rhazes (865-925AD): Wanda Zanen Hotonsa Ne A Kan Wannan Tarihin, Mutumin kasar Farisa (kasar Iran ta yanzu), wanda ya ba da gudunmowar da har a yau ba wanda ya ba da irinta a harkar lafiya. Domin ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya sha kawo bayanai na canjin tunani da hujjoji masu gamsarwa a harkar lafiya. Misali, shi ne wanda ya fara bambance ciwon Agana (mai sa cin zanzana, wanda kuma aka riga aka ga bayanta a yanzu) da Bakon Dauro, wanda duka kwayar cutar birus ce ke kawowa. Shi ne kuma wanda ya kirkiro kayan aikin likita da dama irinsu. Ya rubuta littattafai a kan harkar lafiya fiye da ɗari. Fitacce a cikinsu shi ne ‘Al-Hawi,’ wanda kundin bayanai ne a kan aikin likita da ya shafi magunguna da yadda suke aiki a jikinmu.

A wani shagube da ya taba yi wa wani mai maganin ciwon ido, wanda ya kawo masa magani don ya sa a idonsa, sai ya tambaye shi da ya yi masa bayanin yadda ido ke aiki amma ya kasa, don haka ya ce maganin karya ne. Wannan ne ke mana tuni da taka-tsan-tsan wajen sayen magunguna a wurin jahilai.

Ali Ibn Abbas: Haly Abbas (920-994 AD): Shi ma daga Farisa ya fito kuma ana ji da shi a duniyar likitanci. Ya ba da gudunmuwa ta hanyar rubuta littattafai cikin harshen Larabci, wadanda suka fi bayani a kan bangaren kwakwalwa da cututtukanta da bayanan falsafar binciken kimiyya irin na zamani.

Abul kasim Al-Zahrawi: Abulcasis (936- 1013 AD): Wanda yake Balarabe ne wanda aka haifa a kasar Spaniya. Ya yi fice wajen zama likitan tiyata na farko na zamani a duniyar Musulunci saboda kirkiro kayan aiki na leka wurare da dama na jikin mutum da ya yi, fiye da dari biyu, wadanda daga su ne aka kera na wannan zamani. Shi ne kuma ya fara nuna wa duniya cewa za a iya samun juna biyu a wajen mahaifa saboda tiyatar da ya sha yi a wannan bangare.

Ya zama likitan Khalifan Musulunci a kasar Andalusiya, wato Khalifa Al-Hakam kuma ya rubuta littattafai da dama a kan aikin tiyata, wanda har yanzu akan samu manhajojin a littattafan wannan zamani. Domin karin bayani, za a iya bincikar Kitabut Tasrif.

Abu Ali Ibn Sina: Abicenna (980-1037): Shi ma mutumin kasar Farisa ne, wanda yake da baiwar kaifin hadda da tunani mai zurfi. Ya haddace Alkur’ani yana dan shekaru goma kacal, sa’annan ya zama likita yana dan shekara sha shida. Ya yi aikin duba marasa lafiya kyauta a wannan birni kuma ya zama babban likitan Khalifan garin.

Daga baya ya yi hijra ya nufi yamma, inda a hanya ya rubuta kundaye a kan bayanai na kula da lafiya da aikin likita, ya kuma koyar da dalibai. Wannan kundi wanda ake kira ‘kaanun fid dibb’ an dade ana amfani da shi a jami’o’in kasashen yamma na wancan lokaci, a matsayin littafin koyarwa.

Ga kuma irinsu Ishak Al-Ruhawi dan kasar Turkiya, wanda ya fara bayani a kan tarbiyyar likitoci; wato yin tsantseni da taka-tsan-tsan a kan aikin likita da hukuncin da ya kamata a ba likitoci masu ganganci da aiki a cikin littafinsa mai suna ‘Adab Al-Tabib.’ Shi ne kuma ya fara bayanin cewa kowane sabon abu aka samar a kimiyyar likita, dole a samu wasu kwararru a aikin su zurfafa bincike don tabbatar da sabon bayanin ko karyata shi.

Sai kuma wasu da dama irinsu malaman waɗannan da muka lissafa waɗanda ba su yi fice kamar ɗalibansu ba. Misali, malamin Al Razi, Abu Hassan Al-Tabari, wanda ya yi fice a harkar lafiyar yara.

Akwai kuma irinsu Abu Alhassan Ibn Al-Nafis, likitan kasar Suriya wadanda Turawa ma ba su sani ba ko kuma suka sani amma suka ki ambatonsu. Shi ne wanda ya fara bayanin yadda jini ke zagaya jikinmu, tun kafin ma a haifi Baturen nan William Harbey, wanda suka ce shi ya fara wannan bayani. Da dai sauran ire-irensu.

Post a Comment

Previous Post Next Post