Nestlé Za Ta Sallami Ma’aikata 16,000 Duniya Baki Daya

Kamfanin Nestlé, wanda shi ne mafi girma a duniya wajen sarrafa abinci a fakiti, ya sanar da shirin sallamar ma’aikata 16,000 a faɗin duniya cikin shekaru biyu masu zuwa, a wani shiri na sake fasalin harkokinsa domin ƙara inganci ta hanyar amfani da na’urorin atomatik.

A cewar kamfanin, kusan ma’aikata 12,000 daga cikin masu aiki a ofisoshi da kuma 4,000 daga sashen masana’antu da samar da kayayyaki ne abin zai shafa. Kamfanin ya ce za a gudanar da tattaunawa “inda ya dace,”

kamar yadda sanarwar Alhamis ta nuna.

Nestlé, wadda ke kera kayayyaki irin su Nescafé, Cheerios, KitKat, da Rolos, ta ce wannan mataki na cikin ƙoƙarinta na ƙara “ingantacciyar gudanarwa.” Ana sa ran hakan zai taimaka wajen adana kuɗaɗe kimanin fam miliyan 934 a shekara.

Sai dai har yanzu ba a san yadda wannan mataki zai shafi ayyukan Nestlé a Birtaniya ba. Wani mai magana da yawun kamfanin ya shaida wa Sky News cewa, “A wannan lokaci, ba mu da tabbatattun alkaluma kan kowace ƙasa daban.”

Kamfanin na da masana’antu, cibiyoyin rarraba kaya da ofisoshi a duk faɗin Ingila, Scotland da Wales, amma ya ce bai da takamaiman adadi na ma’aikatansa a Birtaniya. A duniya gaba ɗaya, Nestlé na da ma’aikata kusan 277,000.

Shugaban kamfanin, Philipp Navratil, ya bayyana matakin a matsayin “mai wuya amma wajibi,” yana mai cewa sallamar za a yi ta “cikin mutunci da gaskiya.” Wannan shi ne babban canji na farko da ya jagoranta tun bayan karɓar ragamar kamfanin a watan Satumba, bayan murabus ɗin tsohon shugaban kamfanin, Laurent Freixe.

Navratil ya ƙara da cewa, “Yayin da Nestlé ke tafiya gaba, za mu yi tsauraran matakai wajen rabon albarkatu, muna fifita damammaki da sassan kasuwanci da ke da mafi girman ribar da za a iya samu. Muna ƙarfafa al’adar aiki mai gasa, wadda ba ta yarda da rasa kasuwa ba, kuma inda nasara take samun lada.”


Post a Comment

Previous Post Next Post