Wani babban al'amari da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, kuma yake ta jawo ce-ce-ku-ce a cikin al'umma shi ne sulhu da 'yan ta'adda musamman irin wanda aka yi a Jihar Katsina ganin cewa 'yan ta'addan ba su miƙa makamansu ga Gwamnati ba.
Sanannen abu ne cewa Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin Jagorancin Malam Dikko Umar Radda ta gabatar da sulhu a wasu sassan jihar, inda wasu ƙananan hukumomi suka samu yin zaman sulhu tsakanin su da 'yan bindigar. Daga cikin ƙananan hukumomin da suka gabatar da wannan sulhu, Akwai Faskari, Ƙanƙara, Sabuwa, Ɗandume, Batsari, Jibiya da sauransu. Sai dai wasu mazauna yankin sun bayyana wa wakilin Amsoshi 360 cewar har yanzu 'yan ta'addar sukan ƙwaci wayoyin hannu, babura da kuɗi a hannun mutane.
Ta ɗayan ɓangaren kuwa, an hango Shugaban ƙaramar hukumar Sabuwa, Engr. Sagir Tanimu Sabuwa a wata ruga da ke cikin daji, yayin da ya halarci daurin auren wani ƙasurgumin tubabben ɗan fashin daji, lamarin da ya jawo hankalin gidajen jaridu da kuma kafafen sada zumunta. A fahimtar mutanen yankin, suna ganin cewar yin hakan wani yunƙuri ne na dawo da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al'ummar yankin.
