Gwamna Dauda Lawal Ya Nemi Canjin Fasaha Don Samar Da Gwamnati Mai Hadin Kai A Afirka

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin kai a nahiyar Afrika domin inganta shirin sauyin dijital na nahiyar. Yayin da yake jawabi a taron Digital Government Africa Summit da aka gudanar a Lusaka, Zambia, Gwamna Lawal ya jaddada cewa fasaha “dole ta zama sabon ginshiƙin mulki,” wato ta zama tushen inganta hukumomi, ilimi, da bunƙasar tattalin arziki a fadin nahiyar.
Gwamnan ya bayyana cewa Jihar Zamfara tana bin tsarin Manufar Ƙasa ta Tattalin Arzikin Dijital na Najeriya, inda ya bayyana kaddamar da dandalin e-GovConnect, domin sauƙaƙa ayyukan gwamnati da ƙara gaskiya da ɗa’a a gudanar da harkokin gwamnati. Haka kuma, ya bayyana kafa Cibiyar Fasahar Bayanai ta Zamfara (ZIIT) da shirye-shiryen koyon ilimin dijital domin samar wa ɗalibai da ’yan kasuwa ƙwarewar da ta dace a fannin fasaha.

Lawal ya sanar da cewa Zamfara za ta karɓi bakuncin Arewa Tech Festival, babban taron fasaha mafi girma a Arewacin Najeriya, domin mayar da jihar cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire ta dijital a yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin kare bayanai da tsaron yanar gizo, yana mai cewa “duk wani sauyin dijital dole ne ya ginu ne kan amana.”

A ƙarshe, Gwamna Lawal ya yi kira ga ƙasashen Afrika su faɗaɗa hanyoyin samun intanet mai sauri (broadband), su gina cibiyoyin bayanai masu tsaro, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar yankuna. A cewarsa, “ma’aunin nasara ba yawan tsarin da aka kaddamar ba ne, sai dai yawan rayukan da aka inganta.”

Post a Comment

Previous Post Next Post