Majalisar Koli Ta Kasa Ta Amince Da Naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Kasa (INEC).

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya gabatar da sunan Amupitan ga majalisar yayin taron da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Laraba, bayan karewar wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya fara aiki tun a shekarar 2015 kuma ya ƙare a watan Oktoba 2025.

A cewar wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, Shugaba Tinubu ya bayyana Amupitan a matsayin “malami mai gaskiya kuma marar son kai a siyasa”, tare da jaddada cewa shi ne mutum na farko daga Jihar Kogi, yankin Arewa ta Tsakiya, da aka taɓa ba wannan mukami.

Mambobin Majalisar Koli ta Ƙasa gaba ɗaya sun amince da wannan naɗi, inda Gwamna Ahmed Usman Ododo ya yaba wa ƙwarewa da halayen Amupitan.

Daidai da tanadin doka, Shugaba Tinubu zai aika da sunan Amupitan zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa da tabbatar da shi.

Amupitan, mai shekara 58, Farfesa ne na Dokar Shari’a kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos (bangaren gudanarwa). Ya fito ne daga garin Ayetoro Gbede, Ƙaramar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi, kuma ya zama Lauya Babba (SAN) a shekarar 2014.

Post a Comment

Previous Post Next Post