APC Ta Hana Kayode Ojo Yin Takarar Gwamna A Jihar Ekiti

 

Kayode Ojo

Jam’iyyar APC ta ƙi amincewa da ɗaya daga cikin ƴan takarar gwamnan Jihar Ekiti, Injiniya Kayode Ojo, shiga zaɓen fidda-gwani na jam’iyyar da kuma takarar gwamna.

An sanar da wannan hukunci ne jim kaɗan bayan da Ojo ya ziyarci hedikwatar jam’iyyar da ke Ado-Ekiti a jiya Alhamis, inda shugabannin jam'iyyar su ka hana shi shiga.

A baya, an ruwaito cewa Ojo ya samu rakiyar dubban magoya baya daga kananan hukumomi 16 na jihar yayin da ake dakon ranar zaɓen na fidda-gwani a 27 ga Oktoba.

A cewar wani rahoto daga TVC, an tabbatar da cewa an ƙi amincewa da Kayode Ojo daga shiga takarar gwamna a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post