Zanga-Zangar Rashin Wutar Lantarki Da Ruwa Ta Rikide Zuwa Rikici Tsakanin Matasa Da Hukumomi

 

Zanga-zanga

Daruruwan masu zanga-zanga sun cika titunan Antananarivo, babban birnin Madagascar, domin nuna ɓacin ran su kan matsalar yawan katsewar wutar lantarki da rashin ruwa wanda ke shafar gidaje da kasuwanci tsawon sa’o’i da dama a kullum. Zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali bayan jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa kuka da harsasai na roba don tarwatsa masu zanga-zangar, abin da ya haifar da fasa-ƙasa, kona shaguna, da tashin hankali a wasu sassan birnin.

A sakamakon hakan, gwamnati ta kafa dokar hana fita daga ƙarfe 7 na yamma zuwa 5 na safe, tana mai cewa hakan yana da nufin dawo da zaman lafiya. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun toshe hanyoyi, sun kunna wuta a kan tituna, sannan sun kai hari ga gidajen wasu ‘yan siyasa. Rahotanni sun ce an kona gidajen ‘yan majalisar da ke goyon bayan gwamnati guda uku tare da lalata wasu kadarori na kasuwanci.

Zanga-zangar, wacce ake cewa “Gen Z Movement”, ta samo asali ne daga matasa da suka gaji da cin hanci, talauci, da rashin kulawa daga gwamnati. Masu zanga-zangar sun ƙi karɓar tayin tattaunawa daga gwamnati, suna kuma ci gaba da kira da Shugaba Andry Rajoelina ya sauka daga mulki. Rahotanni sun nuna cewa akwai mutane da dama da suka mutu da kuma raunuka, yayin da jama’a ke ci gaba da neman sauyi na zahiri daga gwamnati.

Post a Comment

Previous Post Next Post