A Bisa Hasashe Ba Lallai Ne A Ba Wa Donal Trump Lambar Girmamawa Ta Nobel Peace Prize Ba

 "A bisa hasashena ba lallai a ba shi ba saboda dalilaina guda uku kamar haka:

1. Su dai masu bayar da wannan Nobel Peace Prize ɗin suna bayar da shi ne bisa wasiyyar wani da ake kira da Alfred Nobel, cewa duk wanda za a ba wannan Prize ɗon dole sai ya samar da zaman lafiya mai ɗorewa, na tsawon lokaci, ba wai sasanci na wucin gadi ba, kamar dai irin na Trump wanda ba tabbas.

Donald J Trump

2. Trump ya saɓa da wata ƙa'ida ta bayar da Nobel Peace Prize ta yadda yakan ɗauki ɓangaranci a kalamansa da ayyukansa, kamar a dambarwar ƴan Palestinawa da Isira'ila da kuma Iran. Wannan ma yana nuna wanda yake son samar da zaman lafiya mai ɗorewa ba zai dinga haka ba.

3. Su wannan kwamiti na Nobel Peace Prize raini a gare su a samu wani ɗan siyasa da zai dinga gaya wa duniya cewa shi fa ya cancanta har ma ya dinga nuna shi fa "dole" a ba shi. Don haka in suka ba shi za a samu wasu ma su dinga kawo irin wannan rainin a gare su. 

Mu dai namu jira ne. Amma in dai aka ba shi to zan rage ganin darajar wannan kwamiti na Nobel Peace Prize saboda ya saɓa ƙa'idojinsu ta fannoni da dama ba wai ma fa iya guda uku ɗin nan da na lissafo ya saɓa ba." In ji Bashir Shu'aibu Jammaje, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.

Post a Comment

Previous Post Next Post