Yan Ta'adda A Jihar Zamfara Sun Kai Farmaki A Garin Yandoton Daji Inda Suka Kashe Jami'an CJTF Uku da Askarawa Biyar

Rashin tsaro, wani lamari ne da ya addabi Arewa maso yammacin Nijeriya duk da cewa Gwamnatin ƙasar na nuna damuwa sosai a kan lamarin. Rahotanni daga Jihar Zamfara sun bayyana cewa,  jiya 09/10/2025  wasu gungun 'yan ta'adda suka kai farmaki a garin 'yan Doton Daji, inda suka kashe Jami'an tsaron JTF har mutum uku, wanda faruwar hakan ya sa jami'an tsaron Askarawa da ke garin Mada suka kai ɗauki gami da yunƙurin ɗauko gawarwakin da 'yan ta'addar suka kashe. Cikin rashin sani, ashe 'yan ta'addar sun yi wa jami'an kwanton ɓauna, hakan ya sa Askarawan suka faɗa Tarkon 'yan ta'addar, inda Suka hallaka Jaruman Askarawa har mutum biyar.

Jami'an Tsaro

Muna Addu'a Gami da Tawassuli da Wannan Rana ta juma'a, Allah ta'ala ya jiƙan waɗannan mujahidai, Ya kuma karɓi Shahadar Su, Ya ƙarfafa Mana Sauran, Ya kuma tsare mana lafiyarmu da rayukanmu, Ya ƙara ɗora mu a kan nasara a duk inda muka dosa, Ya kawo mana ƙarshen wannan masifa ta 'yan ta'adda da masu daukar nauyinsu a yankunanmu da ƙasa baki ɗaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post