A cewar Nwaeke, Dokar Inshorar Lafiya ta Ƙasa ta 2022 ta tanadi cewa duk ma’aikaci a kamfanin da ke da ma’aikata sama da biyar dole ne a haɗa shi cikin tsarin inshorar lafiya.
Ya bayyana cewa Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA) ce ke da alhakin ba da lasisi da sa ido kan ƙungiyoyin Health Maintenance Organisations (HMOs), domin tabbatar da bin ƙa’idoji da samun damar daidaitacciyar kulawar lafiya ga ma’aikata a fannoni biyu gwamnati da masu zaman kansu.
Dan majalisar ya kuma yi bayanin cewa, bisa ga tanadin doka, kamfani na da alhakin biyan kashi 10% na albashin ma’aikaci, yayin da ma’aikaci zai biya kashi 5%, wanda ke zama jimillar kashi 15% na albashin tushe.
Sai dai Nwaeke ya nuna damuwa cewa kamfanoni da dama ba sa yin rijista da tsarin, kuma ba sa biyan gudunmawar da doka ta tanada, abin da ke barin ma’aikata cikin hali na rashin taimako lokacin da suka kamu da rashin lafiya.
Ya ce wannan rashin bin doka na kawo cikas ga manufar gwamnati ta samar da ingantaccen tsarin inshorar lafiya ga dukkan ’yan ƙasa, musamman ma’aikatan da ke fuskantar matsin tattalin arziki.
Daga karshe, Majalisar ta buƙaci Hukumar NHIA da ta fara tattara bayanai kan dukkan kamfanonin da ke karya dokar tare da daukar matakin ladabtarwa a kansu.
Haka kuma ta umarci Kwamitin Majalisa kan Harkokin Lafiya da ya tabbatar da bin wannan doka yadda ya kamata, tare da miƙa rahoto cikin makonni hudu domin ɗaukar ƙarin matakin majalisa.