Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi gargaɗi mai tsanani ga duk wanda ke ƙoƙarin lalata shirin sabunta gine-ginen babban birnin, musamman aikin “Light Up Abuja.”
Gargaɗin na Wike ya biyo bayan wani lamari da ya faru kwanan nan inda fitilun titin hanyar filin jirgin sama suka daina aiki yayin da Shugaba Bola Tinubu ke dawowa Abuja.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da aikin titin Collector Road CN2 — wanda zai haɗa Yemi Osinbajo Way da Wole Soyinka Way a ranar Alhamis, Wike ya ce:
“Na yi dariya, domin tun da farko na riga na faɗa muku cewa za a yi faɗa, amma muna da shirin tunkarar hakan. Idan mutum yana raye, dole ne ya yi faɗa; matattu ne kawai ba sa faɗa.”
Wike ya bayyana cewa ya kira kamfanin CCECC domin neman bayani kan matsalar fitilun, kuma an riga an ba shi cikakken rahoton Ya ƙarfafa duk masu ruwa da tsaki a aikin da su ci gaba da jajircewa, yana mai cewa gwamnatin FCT ba za ta bari a takura mata ba.
“Waɗannan abubuwa duk don su ɓata mana hankali ne, amma ba za su yi nasara ba. Ni da tawagata mun daure sosai, kuma babban aikin da dole ne mu kammala shi ne ‘Light Up Abuja,’” in ji shi.
Ministan ya ce titin da aka ƙaddamar na cikin shirin manyan ayyukan da za a kammala domin bikin cikar shekara uku na mulkin Shugaba Tinubu da kuma cika shekara 50 da kafuwar FCT a shekarar 2026.
Ya bayyana cewa titin zai bai wa sabuwar hanyar Gishiri–Maitama ma’ana, domin a baya ba ta da cikakken haɗi da manyan tituna.
“Ku tuna cewa a watan Yuli bana, Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da gadar nan, amma muka ga cewa idan ba a haɗa wannan hanyar ba, aikin ba zai zama cikakke ba,” in ji Wike.
Wike ya yaba wa kamfanin China Geo-Engineering Corporation (CGC) saboda fara aiki tun kafin a kammala yarjejeniyar kwangila, yana mai cewa hakan alamar amincewa ce da gwamnatin Shugaba Tinubu.
Ya kuma bayyana cewa aikin zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziki ta hanyar ƙara darajar kadarori a yankin.
“Idan kadarar nan tana da darajar miliyan 200 ko 300 a yanzu, cikin wata guda za ta kai miliyan 700 ko har biliyan ɗaya. Wannan shi ne ainihin ma’anar kyakkyawan mulki da cigaba,” in ji shi. Wike ya ƙara da cewa ya ji kansa cikin waɗanda Allah Ya yi wa albarka domin shugabanci a wannan lokaci.
“Mun taɓa zama gwamnonin zinariya, yanzu kuma mun zama ministocin zinariya. Ka ga kenan Allah yana ƙaunarmu sosai,” in ji shi da murmushi.
Sabuwar hanyar Collector Road za ta taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa a yankunan Katampe da Gishiri, tare da shirin kammala aikin kafin cikar shekara uku na mulkin Shugaba Tinubu.