Tarayyar Turai (EU) na shirin amincewa da wata yarjejeniya da za ta ba da dama a fara amfani da dukiyar Rasha da aka ƙwace (frozen assets) domin taimaka wa Ukraine wajen ci gaba da yaƙin da take yi da Rasha.
Rahotanni sun nuna cewa ministocin kuɗi na ƙasashen EU suna gab da kammala shawarwari kan yadda za a tsara tsarin amfani da kuɗaɗen da aka ƙwace daga bankunan Rasha tun bayan da ta kai hari kan Ukraine a shekara ta 2022.
A cewar jami’an EU, wani kaso daga cikin ribar da ake samu daga waɗannan kuɗaɗe za a tura su zuwa asusun tallafin soja da farfaɗo da tattalin arziki na Ukraine.
Wani babban jami’i a hukumar EU ya bayyana cewa: “Wannan mataki yana da nufin tabbatar da cewa Rasha ta biya farashin barnar da ta haddasa a Ukraine, ta hanyar amfani da kuɗaɗenta da aka ƙwace.”
An kiyasta cewa Tarayyar Turai ta ƙwace fiye da euro biliyan 200 na kadarorin Rasha, ciki har da na bankin tsakiya da wasu manyan ’yan kasarta.
Wasu ƙasashen EU kamar Hungary da Slovakia sun nuna damuwa cewa hakan na iya haifar da rikici a fannin doka, amma yawancin ƙasashen Turai suna goyon bayan wannan mataki a matsayin hanyar tallafa wa Ukraine ba tare da amfani da kuɗin jama’a ba.
Masana sun bayyana cewa wannan mataki na EU na iya zama muhimmin mataki a yaƙin tattalin arziki da Rasha, da kuma sabon salo na tallafin yaki ta hanyar amfani da kadarorin da aka ƙwace daga mai farmaki.