Dalilan Da Ke Haddasa Ciwon Ciki A Saman Cibiya

 Ciwon ciki matsala ce babba da ke damun mutane a wannan duniya tamu. Ciwon ciki,  ciwo ne da ke buƙatar kulawa ta musamman, sannan ciwo ne da ya kasu zuwa ɓangare daban-daban. Yana da kyau a ziyarci likita cikin lokaci domin kaucewa matsala babba.

Mai Ciwon Ciki

1. PEPTIC ULCER DISEASE (Ulcer).

Idan "ulcer" tana kusa da tsakiyar ciki (gastric ko duodenal ulcer), ciwon yana bayyana a saman cibiya ko tsakiyar ciki. Ana iya jin ciwo kafin ko bayan cin abinci. Wasu lokuta kuma ana iya jin ciwon yana zuwa da amai ko tashin zuciya.

2.GASTRIC

Yana faruwa idan "acid" na ciki ya fara cinye bangon ciki. Ana jin ciwo mai ƙuna ko mutum ya ji kamar ana hura wuta a saman cibiyarsa. Yawan shan "coffee" da magunguna "painkillers"(NSAIDs), ko "stress" na ƙara ta’azzara matsalar.

3. INDIGESTION (Dyspepsia)

Wannan na faruwa idan abinci baya narkewa yadda ya kamata.

Ana iya jin kumburi, nauyi, da ciwon ciki bayan cin abinci.

4. MATSALAR GALLBLADDER (stones ko inflammation)

Idan ciwon yana faruwa ne a saman ciki, ɓangaren dama bayan cin abinci mai kitse, yana iya zama gallstone. Ciwon yana iya zuwa ne a cikin lokaci kuma yana yaɗuwa zuwa baya ko kafaɗa (Abdominal muscle strain). Wasu lokuta ciwon ba daga cikin hanji ba ne, daga tsokar wajen ne.

"Lafiya Uwar Jiki, Babu Mai Fushi Da Ke" in ji Bahaushe, don haka, duk lokacin da mutum ya ji wani yanayi da bai gane ba a bangaren lafiyarsa, yana da kyau a yi saurin zuwa asibiti domin shawo kan matsalar da wuri.

Post a Comment

Previous Post Next Post