Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Zamfara ta zargi Ministan Tsaron Ƙasa, Dr. Bello Muhammad Matawalle, da mayar da ma’aikatar tsaro ta ƙasa wata cibiyar siyasa maimakon mayar da hankali kan matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Halliru Andi, ya fitar a ranar Alhamis, PDP ta bayyana halayen ministan a matsayin “abin kunya ga ƙasa,” tana zarginsa da yin amfani da Defence House wajen karɓar baƙi da gudanar da tarukan siyasa. Jam’iyyar ta ce wannan dabi’a ba ta dace da nauyin da ke wuyan ministan tsaro ba.PDP ta bayyana cewa abin takaici ne kuma abin ƙin yarda, ganin cewa al’ummomin Zamfara na ci gaba da fama da hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kashe-kashe, amma a gefe guda, ana amfani da ma’aikatar tsaro wajen harkokin siyasa. Ta ce irin wannan mataki na rage wa gwamnati ƙwarin guiwa wajen magance matsalar tsaro.
Sanarwar ta kuma kira Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gargadi Dr. Matawalle domin tabbatar da cewa ma’aikatar tsaro ta ci gaba da kasancewa ba ta da alaƙa da siyasa. PDP ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta hana amfani da wuraren tsaro wajen tarukan siyasa tare da mai da hankali wajen dawo da zaman lafiya a Zamfara da sauran yankunan da ke fama da rikice-rikice.
A ƙarshe, jam’iyyar ta tabbatar da goyon bayanta ga duk wani ƙoƙari na gaskiya da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaro da dawo da zaman lafiya a jihar.