Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Dr. Bilyaminu Umar a matsayin Sakatare na farko na sabuwar Hukumar Kula da Mutane Masu Buƙata ta Musamman a jihar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Suleman Ahmad Tudu, Mai taimaka wa Sakataren Gwamnatin Jihar kan harkokin yaɗa labarai, ya sanya wa hannu, inda aka raba wa ’yan jarida a Gusau.Sanarwar ta bayyana cewa naɗin ya fara aiki nan take. Dr. Bilyaminu, mai shekaru 40, shi ne Babban Likitan Dabbobi (GL 14) a Ma’aikatar Gwamnatin Jihar, kuma yana riƙe da muƙamin Shugaban ƙungiyar ƙasa ta Mutane Masu Buƙata ta Musamman (PWDs) a Zamfara.
Sanarwar ta kuma tunatar da cewa Gwamna Lawal a baya ya naɗa Shugaban Hukuma da mambobi guda shida na dindindin, dukkansu mutane masu buƙata ta musamman. Da wannan sabon naɗi, sanarwar ta ce, an cika tsarin jagorancin hukumar gaba ɗaya.