Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Sabon Shirin Karatun Kan Intanet Ga Dalibai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Inspire Live(s) Online Real-Time Classes, wani sabon shirin karatun kan Intanet da zai bai wa ɗaliban makarantu a faɗin ƙasar damar samun ilimi mai inganci ba tare da tangarda ba.

A cikin wata sanarwa, Daraktar Yada Labarai ta Ma’aikatar Ilimi, Folasade Boriowo, ta ce shirin na da nufin magance ƙarancin malamai da kuma yawan dakatar da karatu a makarantu. Ta ce shirin na tafiyar da manufofin “Renewed Hope” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya tabbatar da cewa an fara aiwatar da shirin, wanda za a faɗaɗa zuwa dukkan ajujuwa daga Primary 1 zuwa SSS 3.

A yanzu haka, dandalin Inspire na gudanar da darussa ga JSS da SSS daga Litinin zuwa Juma’a, 8:00 na safe zuwa 2:30 na rana, inda malamai ƙwararru ke koyarwa ta hanyar Cisco Webex.

Post a Comment

Previous Post Next Post