Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO) ta amince da ba wa wasu makarantun Burkina Faso damar gudanar da jarrabawarta, lamarin da ya faɗaɗa ayyukanta a ƙasashen waje.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yada Labarai na wucin-gadi na hukumar, Azeez Sani, ya fitar a Abuja ranar Lahadi. Ya bayyana cewa hukumar za ta fara gudanar da jarabawar Senior School Certificate Examination (SSCE) da Basic Education Certificate Examination (BECE) a ƙasar ta Yammacin Afirka.Sani ya ce matakin ya biyo bayan ziyarar tantancewa da tawagar hukumar ta NECO ta kai makarantun da aka zaɓa a Burkina Faso domin duba cancantar su.
A yayin ziyarar, tawagar ta binciki ajujuwa, dakunan gwaje-gwaje, dakunan karatu, dakunan kwamfuta, dakunan koyon sana’o’i, ɗakunan jarrabawa, filayen wasanni da tsaron makarantu. Haka kuma sun duba bayanan Continuous Assessment (CA), yawan malamai da yanayin koyarwa gaba ɗaya domin tantance shirye-shiryensu.
Bayan cikakken bincike, makarantun sun samu cikakkiyar lasisin gudanar da jarrabawar SSCE da BECE.
Jakadan Najeriya a Burkina Faso ya shawarci al’ummar Najeriya da ke can su yi amfani da wannan dama ta hanyar rajistar ’ya’yansu domin rubuta jarrabawar NECO.
Shugaban tawagar tantancewar, Uche Ezenwanne, ya ce wannan mataki zai ba da damar ga ɗaliban Najeriya da ke zaune a Burkina Faso su rubuta jarrabawar SSCE da BECE ba tare da komawa Najeriya ba.
Ya ƙara da cewa matakin zai ƙarfafa matsayin NECO a matsayin fitacciyar hukumar shirya jarrabawa a nahiyar Afirka.