Wata gagarumar fashewa da ba a taɓa jin irinta ba ta auku a ramin black hole (ko kuma baƙin rami) mai haɗiye duniyoyi da taurari da ke sararin samaniya, wanda girmansa ya ninka na rana sau miliyan 30.
Masana ilimin samaniya sun gano hasken fashewar bayan wani haske mai cike da tururi ya walƙa kuma ya ɓace nan da nan. Yayin da yake ɓacewar, ƙarfin yanayi ya jawo abubuwa da ƙarfin tsiya zuwa cikin sama da saurin da ya kai gudun kilomita 60,000 cikin daƙiƙa ɗaya.Binciken da aka wallafa a mujallar Astronomy & Astrophysics, ya nuna cewa akwai iska mai haddasa wuta kamar wadda take kusa da rana.
Duk da cewa ana kiran su rami, black hole ba ainahin rami ba ne. Wasu ɓurɓushin abubuwa ne manya-manya amma kuma a wurare ƙanana, kamar yadda hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka Nasa ta bayyana. Suna manne da juna ta yadda ƙarfinsu ba ya barin wani abu ya tsallake su - hatta haske.