Gwamnan jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya ya fice daga jam'iyyar PDP mai adawa tare da komawa jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Gwamna Agbu Kefas ya tabbatar da yankar katin jam'iyyar daga shugaban APC na jihar tasa a yau Lahadi a mazaɓarsa ta Hospital da ke ƙaramar hukumar Wukari."Ba da daɗewa ba, na karɓi katina na jam'iyyar APC daga shugaban jam'iiyya na Mazaɓar Hospital Umaru Tanko," in ji shi. "Na yi farin ciki da kykkyawar tarɓar da shugabanni da 'ya'yan jam'iyyar APC suka yi mani."
Tun a ranar 19 ga watan Nuwamba gwamnan ya yi niyyar komawa APC a hukumance amma ya ce ya ɗaga yin hakan saboda yin garkuwa da ɗalibai mata a jihar Kebbi.
Da wannan mataki nasa, gwamnoni biyar ne suka rage wa PDP mai adawa yayin da take shirin ƙalubalantar APC a babban zaɓe na 2027.