An Gabatar Da Bitar Marubuta Labaran Fim

An Gabatar Da Bitar Marubuta Labaran Fim

A ranar Asabar 13/12/2025 da ta gabata ne aka gabatar da taron horar da marubuta labaran fim 53 na masana'antar Kannywood da ke da cibiya a jihar Kano. Bitar ta gudana ne ƙarƙashin kulawar ma'aikatar Nigeria Film Corporation wadda Darakta Dr. Ali Nuhu yake jagoranta.

An shirya horon ne domin ƙara tantance da ƙwanƙwance gami da ƙara zaburar da marubutan yadda za su rubuta ingantattun labarai kuma ƙayatattu. Har wa yau, taron bitar yana da burin ƙyanƙyashe sabbin marubuta labarai a masana'antar ta Kannywood, waɗanda da yawan waɗanda suka samu halartar bitar, marubuta labarai ne ba na fim ba, bitar ta ba su damar jifar tsuntsu biyu da dutse ɗaya.

Bitar ta gudana ne a ɗakin taron Sarari Media and Telecommunications Hub da ke kan titin jami'ar Northwest da ke Kano. 

Waɗanda suka bayar da bitar sun haɗa da: Manyan marubuta fim da suke aiki a tashar Arewa 24 waɗanda suka ƙunshi: Babban daɗaɗɗen marubuci nan Nazir Adam Salihu da marubuciya kuma Uwar Marayu sannan S.A ta gwamnan Kano AKY Hajiya Fauziyya D. Sulaiman da Sarauniyar raha kuma tsohuwar marubuciya Zuwairiyyah Girei da wani tsohon marubucin labari mai suna Nasir Nid, waɗannan su ne suka jagoranci bayar da wannan bita. Sai kuma Kabiru Yusuf Fagge (Anka) da Nura Nasimat waɗanda suka kula gami da shirya bitar.

Bayan an kammala bitar an bayar da ƙwarya-ƙwaryan gwaji domin washe ƙwaƙwalwa gami da tantance marubutan. An kuma ba su kambun shahadar kammala bita.

Taron ya samu halartar shugaban ma'aikatar Nigeria Film Corporation, Ɗan wasa, Mai shiryawa kuma mai bayar da umarni wato Dr. Ali Nuhu.

Post a Comment

Previous Post Next Post