Kocin Real Madrid, Álvaro Arbeloa, ya Shawarci Trent Alexander-Arnold da ya Bar Kulob Din.

Ɗan wasan mai shekaru 27 ya koma Bernabéu ne a bara a matsayin ɗan wasa kyauta daga Liverpool. Duk da haka, rahotanni sun ce Real Madrid ta biya kuɗin diyya kusan €10 miliyan domin ya samu damar taka leda a gasar Club World Cup.

Alexander-Arnold ya fuskanci fara rayuwarsa a Spain cikin wahala sakamakon matsalolin rauni da suka dame shi. Rashin kasancewarsa cikin koshin lafiya ya hana shi kafa matsayi a cikin jerin ’yan wasan farko a ƙarƙashin tsohon koci Xabi Alonso da kuma sabon koci Arbeloa.

Rahoton ya nuna cewa Arbeloa ya yi wata tattaunawa ta musamman da ɗan wasan, inda ya shawarce shi da ya nemi sabon kulob a kasuwar sayen ’yan wasa ta bazara domin amfanin aikinsa na gaba.

An ce Arbeloa ya bayyana masa cewa ba ya cikin tsare-tsaren dogon lokaci na Real Madrid, kuma shawarar da aka yanke ta ta’allaka ne kawai kan dalilai na wasanni. 

Post a Comment

Previous Post Next Post