Ƙungiyar Gamayyar Marubuta Da Manazarta Waƙoƙin Hausa Sun Shiryar Ƙayatacciyar Gasa A Kan Siyasar 2027

*GASA! GASA!! GASA!!!*
*Gamayyar Marubuta Da Manazarta Waƙoƙin Hausa ta Ƙasa* ta ɗauki aniyar gabatar da ƙwarya-ƙwaryar gasar rubutacciyar waƙar Hausa domin farfaɗo da fikirar da ke cikin rubutattun waƙoƙin na Hausa. An shirya gasar ne a matsayin ta farko, wadda kuma za ta rinƙa zuwa duk bayan watanni uku. Ana da burin samar da kundin waɗannan waƙoƙi domin taskance su a wuri ɗaya nan gaba.

*Ƙa'idojin Shiga Gasar:*
1. Za a ɗora waƙar gasa a shafin Facebook na Gamayyar Marubuta Da Manazarta Waƙoƙin Hausa.
2. Dole wanda zai shiga gasa ya bi (following) wannan shafin domin bibiyar halin da ake ciki game da gasar da sauran ayyukan Gamayya.
3. Dole ne a ɗora waƙa a kan taken (jigon) da aka zaɓa, wato:
*Zaɓen 2027: Arewa Ina Mafita?* 
4. Kada waƙa ta gaza baiti goma sha biyar kuma kada ta wuce baiti ashirin.
5. Dole waƙa ta kasance ƙwar biyar.
6. Dole waƙa ta amsa sunan *Rubutacciyar Waƙar Hausa* ta yadda za ta ƙunshi duk abin da ake buƙata a waƙa.
7. Za a fara ɗora waƙoƙin daga ranar Asabar 24/01/2026 zuwa ranar Asabar 07/02/2026 (wato wa'adin mako biyu daidai).
8. Akwai tikitin shiga gasar da za a yanka a kan kuɗi Naira dubu ɗaya kacal ga duk waƙar da mai ita yake son ta ƙetare zuwa gaban alƙalai. Abun nufi, duk waƙoƙin da za a ɗora a kan shafin wancan na Facebook ba za a tantance waƙa a tura ta ga alƙalai ba sai idan an yankar mata tikiti a kan wancan adadin kuɗi da aka ambata.
*Me za a mora daga gasar?*
1. Wanda ya yi nasara a mataki na farko zai sami awalajar Naira dubu goma sha biyar (₦15,000). Yayin da na biyu zai sami Naira dubu goma (₦10,000). Sai kuma na uku ya sami Naira dubu biyar (₦5000). Daga mataki na huɗu zuwa na goma za su sami shaidar shiga gasar (satifiket), wanda nan gaba zai iya taka rawa wajen ayyukan hukumomi da gwamnatoci. Bayan wannan, akwai kyautar littattafai kamar *Matakan Nazarin Rubutacciyar Waƙar Hausa* na *Sulaiman Salisu Muhammad* da wasu, ga duk waɗanda suka yi nasara daga mataki na ɗaya har zuwa na goma.
2. Za a rinƙa tattara waƙoƙin domin tace su a samar da kundaye matsayin wallafaffu.
Domin ƙarin bayani:
+2348067917740
+2348023717639
+2347060438556

Post a Comment

Previous Post Next Post