Jami'an ƴansanda huɗu da masu gadin bakin teku biyu na fuskantar shari'a a Italiya, kan zargin sakaci wajen nutsewar ƙwale-ƙwalen ƴan ci-rani a shekara ta 2023.
Aƙalla mutum 94 ne suka mutu lokacin da ƙwake-ƙwalen mai cike da mutane ya daki dutse sannan ya rabe gida biyu a cikin tekun Italiya.Yara 35 cikin waɗanda suka rasa ransu.
Masu gabatar da ƙara sun zargi ƴansanda da jami'an kula da bakin teku da ƙasa ceto ƙwale-ƙwalen da fasinjojinsa, duk da cewa an ayyyana musu lokacin da lamarin ke faruwa sa'o'i bakwai kafin jirgin ruwan ya nutse.