Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa an samu kyakkyawan ci gaba a tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka bayan sabuwar ganawa da aka yi. Ya ce ɓangarorin biyu sun fara fahimtar juna kan wasu ƙa’idoji da za su jagoranci ci gaba da tattaunawa, kuma hakan na iya taimaka wajen rubuta yarjejeniyar da za ta warware taƙaddamar nukiliyar Iran.
Sai dai Araghchi ya gargaɗi cewa duk da wannan ci gaba, hakan ba yana nufin yarjejeniya za ta samu nan da nan ba, domin matakin rubuta cikakken yarjejeniya yana da wahala kuma yana bukatar tattaunawa mai zurfi kan cikakkun bayanai. Jami’an Amurka ma sun amince cewa an samu dan ci gaba, amma har yanzu akwai batutuwa masu yawa da suke bukatar warwarewa kafin a kai ga karshe.
Tattaunawar na zuwa ne a lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ke cike da rashin jituwa kan shirin nukiliyar Iran, takunkumi, da kuma barazanar rikici. Masu sa ido na ganin cewa idan aka ci gaba da wannan tattaunawa cikin nasara, zai iya rage tashin hankali a yankin da kuma bude kofar sabuwar yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu.